<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) A cikin zuciyata na ji muryar Mai Cetona.
 &quot;Ka zo gare ni nan&quot;, ta ce, &quot;In ba ka hutawa&quot;.
 Na zo gun Yesu hakanan, da zunubi mai yawa,
 Ya saukar mini fa da su, ya ba ni warkarwa.

[V2]
 2) Muryar ta kuma ce da ni, &quot;Ga ruwan rai na bayar.
 Ka zo, ka sunkuya, ka sha, ka daina ƙishirwa.&quot;
 Na zo gun Yesu fa, na sha daga rijiyar rai.
 Kishi ya ƙare, na natsu, raina ya wartsake.

[V3]
 3) Muryar Mai Cetona ta ce, &quot;Ni hasken duniya ne.
 Wanda ya zo gun haskena, ransa zai tsarkake.&quot;
 Na zo na shiga haskensa, ya rayad da ruhuna,
 Har abada kuwa nan na ke gun Yesu, Sarkina.</lyrics>
<title>A Cikin Zuciyata Na Ji Muryar Mai Cetona LW181</title>
<hymn_number>181</hymn_number>
</song>